CAF: Setif da AS Vita a wasan karshe

CAF Logo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za su fara karawa a cikin watan Oktoba wasan farko

Kungiyar Algeria Entente Setif ta samu kaiwa wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Afirka, duk da do ke ta 3-2 da TP Mazembe ta yi a Jamhuriyar Congo.

TP Mazembe ta yi rashin nasara a Algeria da ci 2-1, jumulla sun tashi wasa 4-4 kuma Setif ta samu kai wa wasan karshe a kofin da ta taba lashewa a 1988.

Setif za ta kara da AS Vita ta Jamhuriyar Congo a wasan karshe, inda Vita ta samu kaiwa wasan karshe bayan da ta do ke CS Sfaxien da ci 2-1 ranar Asabar.

Kulob din Vita ne zai fara karbar bakuncin Entente Setif ranar 26 Oktoba, kafin a buga wasa na biyu a Algeria ranar I ga watan Nuwamba.