Kano Pillars ta doke Lobi Stars 2-0

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Saura wasanni tara a kammala gasar Nigeria Premier

Kungiyar Kano Pillars ta doke Lobi Stars da ci 2-0 a gasar Premier Nigeria wasan mako na 29 da suka fafata ranar Lahadi.

Golan Pillars Joe Afelokai ne ya fara zura wa Lobi kwallo a raga a dukan fenarity, kafin daga baya Azeez Shobawole ya kara kwallo ta biyu a raga.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga, Kaduna United ta doke Gombe United da ci 3-0, yayin da El-kanemi da Sharks suka tashi wasa kunnen doki.

Wasan hamayya tsakanin Enyimba da Heartland ta shi suka yi canjaras, Dolphins ta lashe Nasarawa United da ci 2-1, ita kuwa Enugu Rangers doke Taraba United ta yi da ci daya mai ban Haushi.

Fafatawa tsakanin Warri Wolves da Abia Warriors ruwa ne ya yi kancal, inda alkalin wasa ya hura tashi, sai ranar Litinin za a karasa karawar.

Har Yanzu Kano Pillar ce ke matsayi na daya a teburin Premier da maki 50, bayan kammala wasannin mako na 29, saura wasanni tara a kammala gasar Premier Nigeria.

Ga sakamakon wasanni mako na 29 da aka buga:

Dolphin 2 vs 1 Nasarawa United El-Kanemi Warriors 1 vs 1 Sharks Enugu Rangers 1 vs 0 Taraba FC Enyimba FC 0 vs 0 Heartland Giwa FC 2 vs 0 Bayelsa United Kaduna United 3 vs 0 Gombe United Kano Pillars 2 vs 0 Lobi Stars Nembe City FC 1 vs 1 Crown FC Sunshine Stars 0 vs 0 Akwa United Warri Wolves vs Abia Warriors