Van Gaal: Rooney ya cancanci kora

Wayne Rooney
Image caption karo na shida kenan Rooney yana samun jan kati a wasa

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce, Wayne Rooney ya cancanci jan katin da a ka bashi a karawar da suka do ke West Ham da ci 2-1 ranar Asabar.

Alkalin wasa Lee Mason ne ya kori Rooney a gasar Premier da suka kara da West Ham a wasan mako na biyar.

Hakan na nufin Rooney ba zai buga wasanni uku ba, ciki har da karawar da za suyi da Chelsea, kuma jumulla ya karbi jan kati karo shida kenan tun da ya fara buga tamaula.

Rooney, ya samu jan kati daya lokacin da yake kwallo a Everton, sannan ya samu guda biyu a wasanni da tawagar kwallon Ingila.

Jan katin da ya karba na karshe shi ne wanda aka ba shi a karawa tsakanin Ingila da Montenegro a shekarar 2011, sai kuma a United a fafatawar da suka yi da Fulham a Old Trafford a 2009.