AFCON 2015: Nigeria ta gayyato Moses

Victor Moses Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Moses ya dawo kan ganiyarsa a Stoke City

Nigeria ta gayyato Victor Moses cikin tawagar 'yan wasan da za su buga mata da Sudan a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afirka na badi.

Moses mai wasa a Stoke City, rabon da ya buga wa Super Eagles wasa tun karawar da Faransa ta do ke Nigeria 2-0 a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Nigeria ta kuma gayyato mai wasan tsakiya Raheem Lawal da Michael Babatunde da Hope Adam da ke wasa a Reading da Samuel Emmanuel da Aaron Samuel da Ugonna Anyora.

Super Eagles za ta kara da Sudan ranar 11 ga watan Oktoba, kafin ta karbi bakuncin wasa na biyu a Abuja kwanaki hudu tsakani.

Ga jerin sunayen 'yan wasan da aka gayyato Super Eagles.

Masu tsaron raga: Vincent Enyeama (Lille, France); Austin Ejide (Hapoel Be'er Sheva, Israel); Chigozie Agbim (Gombe United).

Masu tsaron baya: Elderson Echiejile (Monaco, France); Juwon Oshaniwa (Ashdod FC, Israel); Efe Ambrose (Celtic FC, Scotland); Godfrey Oboabona (Rizespor FC, Turkey); Azubuike Egwuekwe (Warri Wolves); Kenneth Omeruo (Middlesbrough, England).

Masu wasan tsakiya: John Mikel Obi (Chelsea, England); Ogenyi Onazi (Lazio, Italy); Nosa Igiebor (Maccabi Tel Aviv, Israel); Sone Aluko (Hull City, England); Hope Akpan (Reading, England); Raheem Lawal (Eski?ehirspor, Turkey); Ugonna Anyora (FK Haugesund, Norway), Babatunde Michael (Volyn Lutsk, Ukraine).

'Yan wasan gaba: Ahmed Musa (CSKA Moscow, Russia); Emmanuel Emenike (Fenerbahce, Turkey); Gbolahan Salami (Warri Wolves); Osaguona Ighodaro (Enugu Rangers); Victor Moses (Stoke City, England); Aaron Samuel (Guangzhou R & F, China); Sunday Emmanuel (SV Grödig, Austria).