Stoke City ta doke Newcatle da ci 1-0

Stoke vs Newcastle Hakkin mallakar hoto AP
Image caption sakamakon wasan ya saka Pardew cikin tsaka mai wuya

Stoke City ta doke Newcastle da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na shida da suka kara a filin wasa na Britannia ranar Litinin.

Peter Crouch ne ya zura kwallo da kai a dukan da Victor Moses ya yi masa a mintuna 14 da fara tamaula.

Kiris ya rage Stoke ta samu fenariti lokacin da Yoan Gouffran ya yiwa Moses keta a cikin da'ira 18 din Newcastle.

Dan wasan Stoke Marko Arnautovic ya kai mummunan hari sai dai kwallon ta daki turke, shima dan wasan Newcasle Jack Colback ya kai hari daf a tashi wasa.

Da wannan sakamakon Stoke City tana matsayi na 11 da maki takwas bayan kammala wasannin mako na shida, yayin da Newcastle ke mataki na 19 da maki uku kacal.