Ramsey ba zai buga wa Wales wasa ba

Aaron Ramsey Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ramsey zai yi jinyar mako daya kafin ya dawo tamaula

Aaron Ramsy ba zai buga wa Wales wasannin da za ta yi da Bosnia-Hercegovina da Cyprus a neman tikitin shiga gasar kofin Nahiyar Turai a watan Oktoba ba.

Ramsey, dan kwallon Arsenal mai shekaru 23 zai yi jinyar mako guda, bayan ya ji rauni a wasan hamayya da suka tashi 1-1 da Tottenham ranar Asabar.

Kocin Wales Chris Coleman, ba shi kuma da tabbacin ko dan kwallon Liverpool Joe Allen zai murmure ya kuma buga masa karawar.

Allen tsohon dan kwallon Swansea mai shekaru 24, rabon da ya buga wa Wales wasa tun karawar da suka doke Andorra 2-1 ranar 9 ga watan Satumba.

Wales za ta karbi bakuncin Bosnia da Hercegovina a filin wasa na Cardiff ranar 10 ga watan Oktoba, sannan ta ziyarci Cyprus kwanaki uku tsakani.