Manchester City da Roma sun tashi 1-1

Francesco Totti Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tsohon dan wasan da ya zura kwallo a gasar cin kofin zakarun Turai

Manchester City sun tashi wasa kunnen doki da kulob din Roma a gasar cin kofin zakarun Turai da suka fafata a filin Ettihad ranar Talata.

Sergio Aguero ne ya fara zura wa City kwallo a raga a mintuna na hudu da fara tamaula a dukan fenariti da Maicon ya yi masa keta cikin da'ira ta 18.

Maicon ya samu damar farke kwallon da ya buga ta doki turke, kafin daga baya Totti mai shekaru 38 ya farke kwallo ya kuma karya tarihin Ryan Giggs na tsohon dan wasa da ya ci kwallo a gasar.

Manchester City za ta ziyarci CSK Moscow a wasa na uku cikin watan Oktoba, yayinda Roma za ta karbi bakuncin Bayern Munich a Italiya.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

CSKA 0 vs 1 Bayern Mun Apoel Nic 1 vs 1 Ajax Paris St G 3 vs 2 Barcelona Schalke 1 vs 1 NK Maribor Sporting 0 vs 1 Chelsea BATE Bor 2 vs 1 Ath Bilbao Shakt Donsk 2 vs 2 FC Porto