Ander Herrera zai yi jinyar makonni

Ander Herrera Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya shiga jerin 'yan wasan United dake jinya

Dan kwallon Manchester United Ander Herrera zai yi jinyar rauni tsawon makonni, bayan ya karya hakarkarinsa a wasan da suka doke West Ham 2-1.

Dan wasan mai shekaru 25, ya koma United ne daga Athletico Bilbao har ma ya buga mata wasanni hudu inda ya zura kwallo a raga.

Herrera ya shiga jerin 'yan kwallon United da ke jinyar rauni da suka hada da Michael Carrick da Phil Jones da kuma Ashley Young.

Haka kuma kyaftin Wayne Rooney ya samu jan kati, lamarin da ya sa ba zai buga wasanni uku ba, ciki har da karawa da Chelsea.

United za ta kara da Everton ranar Lahadi daga nan ta kara da West Brom da Chelsea da kuma Manchester City.