NFL: An hukunta dan wasa saboda sujjada

Husain Abdullah Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya ce mahukunta ba su sanar da shi sun hukunta shi ba

An hukunta Husaini Abdullah a gasar kwallon zari ruga ta Amurka wato NFL saboda ya yi sujjada a lokacin da ya ci kwallo a wasa.

Abdullah ya ci wa Kansas City Chiefs kwallon ne a karawar da suka doke New England Patriots da ci 41-14.

Dokar wasan NFL ta hana dan wasa yin murnar cin kwallo lokacin da yake zaune ko kwance a fili, amma ba'a hana dan wasa faduwa a kasa ba.

Abdullah, mai shekaru 29, ya sanar da kafafen yada labarai cewa mahukuntan wasan ba su ce masa komai ba a wasa, amma kocinsa ya sanar da shi an hukunta shi nan take.

Mabiya wasan NFL sun bayyana a shafin sada zumunta na intanet cewa 'yan wasa kiristoci sau da dama suna bikin cin kwallo da yin nuni alamar gicciye ta addininsu kuma ba a yi musu komai.

Dan wasan mai bin addinin musulunci sau da kafa bai buga gasar 2012, lokacin da ya tafi aikin hajji tare da dan uwansa shi ma mai wasan kwallon zari rugar Amurka.