Arsenal ta doke Galatasaray 4-1

Arsenal win Galatasaray Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Welbeck ya zura kwallaye uku a raga a karon farko a Arsenal

Arsenal ta doke Galatasaray ta Turkiya da ci 4-1 a gasar cin kofin Zakarun Turai wasa na biyu na rukuni rukuni da suka kara a Emirates ranar Laraba.

Danny Welbeck ne ya fara zura kwallo a ragar Galatasary a mintina na 22 da fara tamaula, ya kuma kara ta biyu saura minti 15 a tafi hutun rabin lokaci.

Arsenal ta kara kwallo ta uku ta hannun Alexis Sanchez daf da a tafi hutun rabin lokaci, yayin da Welbeck ya kara kwallo ta uku a raga a mintuna na 52.

Kwallaye ukun da Welbeck ya ci a wasan, shi ne karonsa na farko da ya zura kwallaye uku rigis a raga tun lokacin da ya zamo kwararren dan wasa.

Galatasaray ta zare kwallo daya tilo a raga ta hannun Burak Yilmaz a bugun fenareti, bayan da golan Arsenal Wojciech Szczesny ya yi keta aka ba shi jan kati.

Arsenal da ke rukuni na hudu wato group D, ta hada maki uku daga cikin wasanni biyu da ta buga a gasar bana.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Atl Madrid 1 vs 0 Juventus Malmö FF 2 vs 0 Olympiakos FC Basel 1 vs 0 Liverpool Ludo Razgd 1 vs 2 Real Madrid Zenit St P 0 vs 0 Monaco Bayer Levkn 3 vs 1 Benfica Anderlecht 0 vs 3 Bor Dortmd