Gyan ya ce anci zarafinsa a kwallo

Asamoah Gyan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gyan ya ce ya harzuka da kalaman da aka fada masa

Dan kwallon Ghana Asamoah Gyan ya zargi dan wasan kulob din Al Hilal Mihai Pintilii da cewar ya ci zarafinsa a wasan cin kofin Zakarun Asia da suka kara ranar Talata.

Gyan ya ce an kira shi da munanan kalamai ne, lokacin da alkalin wasa ya bashi jan kati a ketar da ya yiwa Salem Al-Dawsari.

Pintilii dan kwallon Romaniya mai shekaru 29, ya nufi Gyan a fusace kamar zai doke shi, abin da ya janyo hatsaniya tsakanin 'yan wasan kungiyoyin.

Kulob din Gyan Al Ain ne ya fara lashe karawar farko da ci 2-1, amma aka cire su da yawan kwallaye 4-2 jumulla a karawa biyu da su ka yi.

Kulob din Al Ain ya ce zai rubuta wa hukumar kwallon kafar Asiya korafi, bayan ya kammala tara shaidun da zai gabatar.