Rodgers ya ce Sturridge bai murmure ba

Sturridge and Rodgers Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rodgers ya ce dan kwallon bai samu sauki ba

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya gargadi Daniel Sturridge cewa bai gama samun sauki ba da zai buga wa Ingila wasan neman shiga gasar cin kofin Turai a badi ba.

Sturridge, mai shekaru 25, ya ji rauni ne a lokacin da yake wasan atisaye da tawagar 'yan kwallon Ingila.

Dan wasan bai buga karawar da Liverpool ta yi da FC Basel a gasar cin kofin Zakarun Turai ba, sai dai zai buga wasan Premier da West Brom ranar Asabar.

Rodgers ya ce "idan kasa za ta gayyato dan wasa ya buga mata tamaula tana la'akari da kwazonsa da lafiyarsa, saboda haka Sturridge bai murmure ba.

Kocin ya zargi Ingila da yin wasa rai-rai da dan wasan lokacin da ya ji rauni a filin atisaye kafin ta kara da Switzerland a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai.