Benteke zai buga wa Villa wasa Asabar

Christian Benteke Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Benteke ya ji rauni ne tun cikin watan Afrilun bana

Christian Benteke zai buga wa Aston Villa wasa ranar Asabar a karawar da za tayi da Manchester City a gasar Premier, bayan da ya kammala jinyar da ya yi.

Benteke, mai shekaru 23, ya ji rauni ne tun cikin watan Afirilu, bayan da ya gamu da karaya.

Dan wasan ya komo atisaye makonni biyu da suka wuce, har ma ya zura kwallo a karawar da ya buga wa 'yan wasan Villa masu shekaru kasa da 21.

Dan kwallon Belgium ya zura kwallaye 34 daga cikin wasanni 67 da ya buga wa Villa tun lokacin da ya koma kungiyar a Agustan 2012.

Aston Villa za ta karbi bakuncin Manchester City a filinta na Villa Park a gasar Premier wasan mako na 7.