Platini ya bukaci a wallafa binciken cin Hanci

Michel Platini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Platini ya ce ya kamata a wallafa binciken cin hancin ga jama'a

Shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini ya yi kira ga FIFA data wallafa binciken cin hanci da aka gudanar dangane da bada toshiyar baki kan karbar bakuncin gasar cin kofin Duniya.

Tun a baya Shugaban FIFA Sepp Blatter ya yi watsi da kiraye-kirayen da aka yi na cewar a wallafa bincikin da lauyan Amurka Michael Garcia ya yi kan zargin cin hanci a hukumar.

Platini ya ce "Bani da hannu kan binciken da kuma shawarwarin da lauyan ya bayar, kuma abu ne mai kyau a sanar da masu ruwa da tsaki kan harkar kwallon kafa".

Tuni dai wani lauyan Jamus Hans-Joachim Eckert ya fara bitar binciken cin hancin a FIFA, domin ya fayyace abubuwan da binciken ya zakulo da kuma bada shawara a watan Nuwamba mai zuwa.

A shekarar 2010 ne aka bai wa Rasha izinin karbar bakuncin gasar cin kofin Duniya na shekarar 2018, Qatar kuma ta karbi bakuncin gasar shekarar 2022.