Hodgson: Babu rashin jituwa da Liverpool

Roy Hodgson Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya ce babu rashin jiyuwa tsakaninsa da kocin Liverpool

Kocin tawagar 'yan wasan Ingila Roy Hodson ya ce babu wata rashin jituwa tsakanisa da Liverpool kan batun raunin Daniel Sturridge.

Sturridge, mai shekaru 25, baya cikin 'yan wasan da Ingila ta gayyato, sakamakon jinyar rauni da yake yi.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya soki Ingila da yin wasa rai-rai da raunin da Sturridge ya ji, har ma ya bukaci kada Ingila ta gayyace shi karawar da za suyi da San Marino da Estonia.

Hodgson ya ce "Ban gayyaci Sturridge tawagar yan wasanmu ba saboda jinyar rauni da yake yi".

Sturridge na fama da jinyar rauni da ya hana shi buga wa Liverpool wasanni a baya, amma kila ya buga wa kulob din karawar da za su yi da West Brom a Premier ranar Asabar.

Amma Rodgers ya ce dan kwallon ba zai iya buga wa Ingila wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da za ta kara da San Marino da Estonia a cikin watan Oktoba ba.