'Ko anini ba zan sake asara kan Hull ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Allam ya ce ba za su yi nasara ba idan kungiyar ta ci gaba da amsa Hull City Association Football Club Tigers Ltd.

Mai kungiyar Hull City Assem Allam ya ce ba zai sake kashe wa kulob din ko anini ba, sai ya yi nasara a karar da ya daukaka ga Hukumar kwallon Ingila don sauya sunan kungiyar zuwa Hull Tigers.

Assem Allam, mai shekaru 75, ya yi imani cewa sauya sunan zai kara wa kungiyar kwarjini a idon duniya.

Mai kulob din wanda ya gaza yin nasara a shari'ar farko kan yunkurin sauya sunan a watan Afrilu ba, ya ce ba zai ci gaba da barnar kudi ba, sai ya tabbatar da samun riba.

Ya ce ba muradinsa ne ya sayar da kungiyar da ya yi ta dawainiya da ita tun shekara ta 2010 ba, amma dai yana jin cewa ba shi da zabi.

Allam ya ce kungiya tana bukatar kwarjini kafin ta iya samun karbuwa a duniya, don haka akwai bukatar takaita sunan kungiyar kamarsu Coca-Cola, Twitter da Google.