Moses ba zai buga wasan share fage ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Victor Moses bai buga wa Super Eagles ba tun bayan Gasar Kofin Duniya

Dan wasan gaba na Nigeria, Victor Moses, ba zai buga wasan neman gurbi a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka da kasarsa za ta buga da Sudan a wannan watan ba. Dan wasan ya fama wani rauni ne da ya yi a cinya.

Dole ta sa dan wasan, mai shekaru 23, ya fice daga fili bayan minti 18 kacal a wasan da Stoke City ta sha kashi a hannun Sunderland da ci uku da daya ranar Asabar.

Kocin Nigeria mai rikon kwarya, Stephen Keshi, ya gayyato dan wasan Dolphins, Emem Eduok, don ya maye gurbinsa.

Kocin Stoke, Mark Hughes, ya ce za a tura Moses don a yi masa karin gwaje-gwaje a lokacin hutun wasannin kasa-da-kasa.

Wannan rauni dai wani babban koma-baya ne ga Moses, wanda bai buga wa Super Eagles wasa ba, tun bayan da Faransa ta lallasa su a Gasar Cin Kofin Duniya a Brazil.

Karin bayani