Ana tunanin buga wasan Premier a wata kasar

Premier League Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hakan zai bai wa magoya bayan kungiyoyin Premier kallon wasa kai tsaye

Mahukuntan gasar cin kofin Premier ta Ingila na tunanin buga wasu daga cikin manyan wasannin Premier a wata kasar a kakar wasa ba a Ingila ba.

Tun a shekarar 2008 aka shirya kungiyoyin Premier za su iya fafatawa a tsakaninsu a wata kasar bayan kammala gasa, wanda hakan ya haifar da korafe korafe masu yawa.

A yanzu kungiyoyin Premier sun fuskanci alfanun buga wasan Premier a wata kasar, maimakon karawa a atisayen tunkarar gasa.

Har yanzu ana ta tattaunawa a kan yadda za a tsara buga wasu daga cikin wasannin Premier a wasu kasashen, amma za a dauki tsawon lokaci kafin a yanke hukunci.

Sai dai mataimakin shugaban FIFA, Jim Boyce ya ce hukumar FIFA ta fi sha'awar kowacce gasa a buga ta a kasar da ake fafatawa.