Euro2016: 'Zan yi murna idan muka samu zuwa'

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bale na fatan Wales za ta samu tikin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai

Gareth Bale ya ce zai yi murna idan Wales ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin Nahiyar Turai, tamkar lashe kofin zakarun Turai ne da ya yi da Real Madrid a shekarar 2014.

Wales za ta karbi bakuncin Bosnia-Hercegovina ranar 10 ga watan Oktoba da kuma Cyprus kwanaki uku tsakani a Cardiff.

Bale, mai shekaru 25 ya ce zai yi matukar murna da farin ciki idan kasarsa ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin Nahiyar Turai wanda Faransa za ta karbi bakunci.

Wales tana rukunin da ya kunshi Bosnia-Hercegovina da Belgium da Israel da Cyprus da kuma Andorra hakan ya sa take hangen samun tikiti.

Rabon da Wales ta buga babbar gasa tun 1958, lokacin da Brazil ta doke ta da ci daya mai ban haushi a wasan daf da na kusa da karshe na cin kofin duniya a Sweeden.