'Zaman Ronaldo daram a Madrid'

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ronaldo zai ci gaba da wasa a Real Madrid

Jorge Mendes mai kula da wasan Cristiano Ronaldo ya ce dan wasan ba zai koma Manchester United ba.

Hasali ma, Mendes ya kara da cewa Ronaldo zai ci gaba da buga tamaula a Madrid ne har ya yi ritaya.

Tun a baya an yi ta rade-radin cewa dan wasan zai koma kungiyar United da kwallo a kan kudi fam miliyan 80.

Ronaldo ya koma Madrid ne daga kulob din United a shekarar 2009 a kan kudi fam miliyan 80.

Kocin United Louis van Gaal ya fada a watan jiya cewa yana son dauko dan wasan, amma baya tunanin Real Madrid za ta amince ta sayar masa.