Ferguson ya goyi bayan salon Van Gaal

Sir Alex Ferguson Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Ferguson ya ce ya goyi da bayan shirye-shiryen Van Gaal a United

Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce kokarin Louis van Gaal na gina sabuwar United a Old Trafford ya yi dai-dai.

Ferguson ya ce yana goyan bayan yadda kocin yake gudanar da aikinsa, ya kuma kara da cewa yana da kwarewar da zai iya fuskantar duk wani kalubale.

Van Gaal ya kashe sama da fam miliyan 150 wajen dauko sabbin 'yan wasa, ciki har da Angel Di Maria a matsayin dan wasa mafi tsada a Birtaniya.

Haka kuma United ta rabu da 'yan kwallo 14, ciki har da Danny Welbeck wanda ya koma Arsenal kan kudi fam miliyan 16.

Ferguson ya yi ritaya daga United a watan Mayun 2013, inda David Moyes ya maye gurbinsa, bayan watanni 10 kuma aka sallame shi daga aiki.