'Bale zai iya yin fice kamar Messi'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bale, mai shekaru 25, ya taras da Ronaldo a Real Madrid da ya je kungiyar bara a kan fam miliyan 85

Golan Bosnia-Hercegovina, Asmir Begovic ya ce Gareth Bale yana iya yin fice kamar Lionel Messi da Christiano Ronaldo.

Bale bai taba cin ragar Begovic a yunkuri guda biyar da ya yi a baya ba, yayin da golan ke kokarin hana tauraron na kasar Wales cin kwallo a wasan samun cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Turai a Juma'ar nan a Cardiff.

Golan na kungiyar Stoke mai shekara 27, ya ce ai ba sai an fada ba, Messi da kuma ga alama Ronaldo, su ne 'yan wasa biyu mafi yin fice a duniya yanzu, kuma Gareth Bale na kokarin kamo su.

Haka kuma, kocin Wales, Chris Coleman ya yi imani cewa Bale na iya kwace kambun Ian Rush gwarzon dan wasan da ya buga wa kasar wasanni 73, ya zama mafi ci mata kwallo har guda 28.

Bale ya ci kwallaye 14, 11 daga ciki a wasanni 16 da ya buga har da kwallon da ya ci Andora a wasansu na zuwa Euro 2016 da Andorra.