Euro 2016: Anya za a je da Spaniya?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba ta taka rawar a-zo-a-gani ba a gasar cin kofin duniya ta Brazil

Zakarun Turai, Spaniya ta yi rashin nasara a wasan samun cancantar shiga wata gasa karon farko a cikin shekaru takwas, inda tsohon dan wasan Chelsea Miroslav Stoch ya taimaka wa kasarsa samun gagarumar galaba a kanta.

Iker Casillas ne ya yi kuskuren fahimtar bugun tazara daga ratar yadi talatin na Juraj Kucka, yayin da Slovakia da ke karbar bakunci ta jagoranci karawar a rukuni na uku na zuwa gasar Euro 2016.

Paco Alcacer ya farkewa Spaniya amma Stoch ya sake jefa kwallo da kai, bayan Michal Duris ya kwaso ta.

'Yan kallo sun barke da sowa bayan an busa tashi, yayin da Spaniya, wadda ta lallasa Italiya ci 4 da nema a karawar karshe ta gasar Euro 2012, ta yi rashin nasara karon farko a wasannin cin kofin duniya da na samun damar zuwa gasar Zakarun Turai.

Spaniya wadda za ta je Luxembourg ranar Lahadi, tana da maki uku a wasanni biyu da ta buga, Slovakia kuma na jagorantar rukunin daga nasarar karawa biyu da ta yi.

A wasu wasannin kuma, kasashen Lithuania da Slovenia da ke rukuni daya da Ingila duk sun yi nasara a wasanninsu.

Sweden ta yi canjaras 1 da 1 da Russia a rukuni na 7.

Austria ma ta yi nasara 2 da 1 a wasan da ta kara a gidan Moldova.

Ukraine ta cinye Belarus 2 da nema a rukuni na 3, Macedonia da Luxembourg an tashi 3-2.

Montenegro sun yi kunnen doki da Liechtenstein.