Ebola: CAF ta ki amince wa Morocco

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kwayar cutar Ebola

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta ki amincewa da bukatar Morocco da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 2015 ta neman dage ranakun gasar saboda fargabar yada wa jama'ar kasarta cutar Ebola.

CAF ta ce za a gudanar da gasar ta makwanni uku tsakanin ranakun 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu kamar yadda aka tsara a MOroccon.

A ranar Asabar aka cigaba da wasannin rukuni-rukuni na neman cancantar zuwa gasar inda Sudan ta kara jefa Najeriya mai rike da kofi tsaka-mai-wuya da ci daya mai ban haushi a Sudan din.

Algeria kuwa ta bi Malawi gida ne ta ci ta 2-0 kamar yadda Afrika ta Kudu ta ci Congo Brazaville.

Kasar Ivory Coast kuwa ta bi Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo ne har gida ta lallasa ta 2-1, yayin da Saliyo ta ba da mamaki inda ta bi Kamaru har Yaounde suka tashi canjaras ba ci (0-0).

Togo kuwa ta rikita wa Uganda lissafi ne da ta bita har Kampla ta yi mata daya mai ban haushi.

A ranar Laraba 15 ga watan Oktoba za a yi karo na biyu na wasannin.