An fara gasar cin kofin Afirka ta Mata a Namibia

2014 AWC
Image caption Nigeria ta casa Ivory Coast da ci 4-2 ranar Asabar

Nigeria da mai masaukin baki Namibia sun fara gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta mata da kafar dama domin samun gurbin shiga gasar cin kofin Duniya da Canada za ta karbi bakunci a badi.

A wasan 'yan rukunin farkon da suka buga ranar Asabar Namibia ta doke Zambia da ci 2-0, yayin da Nigeria mai rike da kofin karo shida ta lallasa Ivory Coast da ci 4-2.

Nigeria tana matsayi na daya a teburi sai Namibiya a mataki na biyu, yayin da Ivory Coast wadda ta ke matsayi na uku za ta kara da Namibia ranar Talata.

Ranar Lahadi Afirka ta kudu za ta kara da Kamaru a wasan 'yan rukuni na biyu a filin wasa na Independence da ke Windhoek, sai karawa tsakanin Ghana da Algeria.

Kasashe uku ne za su wakilci Afirka a gasar cin kofin Duniya ta Mata da Canada za ta karbi bakunci daga 6 ga watan Yuni zuwa 5 ga watan Yulin 2015.

Nigeria ce kasa tilo daga Afirka da take halartar gasar cin kofin duniya ta mata tun daga shekarar 1991.