Ingila ta doke Estonia da ci 1-0

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ingila ce ke matsayi na daya a teburi na biyar da maki uku

Ingila ta doke Estonia har gida da ci daya mai ban haushi a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci.

Kyaftin din Manchester United Wayne Rooney ne ya zura kwallo a raga a minti na 73 a bugun tazara, kuma kwallonsa ta 43 da ya ciwa Ingila a tamaula.

Ingila wadda take matsayi na daya a teburi bayan buga wasanni uku tana da maki tara, sai Lithuania a matsayi na biyu da maki shida, inda Slovenia ke mataki na uku da maki uku.

Ingila za ta karbi bakuncin Slovenia ranar 15 ga watan Nuwamba a filin wasa na Wembley.

Ga sakamakon wasu daga cikin wasannin da aka buga:

Ukraine 1 - 0 Macedonia Austria 1 - 0 Montenegro Russia 1 - 1 Moldova