2014 Fifa Club World Cup: An raba jaddawali

FIFA Club World Cup Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ranar 20 ga watan Disamba za a buga wasan karshe

An raba jaddawalin fara gasar cin kofin zakarun Nahiyoyi na badi da Morocco za ta karbi bakuncin a cikin watan Disamba.

Duk kungiyar da ta kasance zakarar kofin Afirka tsakanin AS Vita ta Jamhuriyar Congo da Entente Setif ta Algeria za ta kara da wadda ta samu lashe wasan cike gurbi tsakanin Moghreb Athletic ta Morocco da Auckland City FC ta New Zealand.

Duk kulob din da ya samu nasara a tsakaninsu zai kuma buga wasan gaba da kulob din San Lorenzo na Argentina.

Cruz Azul ta Mexico za ta fafata da wadda ta samu nasara a karawa tsakanin Sydney Wanderers ta Australia ko kuma Al Hilal ta Saudia a wasan neman zakarar Nahiyar Asia.

Nan ma duk wadda ta yi nasara za ta fuskanci zakarar Nahiyar Turai wato Real Madrid a wasan kusa dana karshe.

Za a fara wasannin ne ranar 10 zuwa 20 ga watan Disamba a filayen wasa na Rabar da Marrakech.

Ga yadda jaddawalin wasannin suke: 10 December - Moghreb Tétouan (Morocco) vs Auckland City (New Zealand)

Wasan daf dana kusa da karshe:

13 December - African champions (Entente Setif ko AS Vita Club) vs Moghreb Tétouan/Auckland City

13 December - Cruz Azul (Mexico) vs Asia champions (Western Sydney Wanderers or Al-Hilal)

Wasannin kusa da karshe:

16 December - Real Madrid (Spain) vs Cruz Azul/Asian champions

17 December - San Lorenzo (Argentina) vs Moghreb Tétouan/AucklandCity/African champions

Wasan karshe: 20 December - a filin wasa na Marrakech