Keshi na neman afuwar 'yan Nigeria

Steven Keshi
Image caption Keshi ya ce Nigeria za ta iya lashe wasanninta uku na gaba

Kocin Super Eagles Stephen Keshi ya nemi afuwar 'yan Nigeria saboda kasa taka rawar gani a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta badi.

Nigeria ta sha kashi a hannun Sudan da ci daya mai ban haushi a karawar da su ka yi a Khartoum ranar Asabar.

Keshi ya ce wannan shi ne karonsa na farko da ya nemi afuwa daga magoya baya tun daga lokacin da yake buga tamaula har yanzu da yake kocin tawagar 'yan wasan saboda kasa taka rawar gani.

Kocin ya shaida wa 'yan wasa cewa su kara zage damtse domin lashe wasanni uku da ke gabansu da zai basu damar kare kambunsu a Morocco a badi.

Nigeria wadda ke rukunin farko ta samu maki daya kacal daga wasanni ukun data buga abin da yasa take matsayi na hudu, Inda Afirka ta kudu ke matsayi na daya da maki 7 sai Congo da maki 6 yayin da Sudan ke da maki 3.

Super Eagles za ta karbi bakuncin Sudan a wasa na biyu a katafaren filin wasa na babban birnin tarayya da ke Abuja ranar Laraba.