FIFA: Garcia ya yi Allah wadai da jami'ai

FIFA Logo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Blatter ya nace kan baza a wallafa rahoto kan binciken cin hanci ba

Lauya mai kula da tarbiya da da'ar ma'aikatan FIFA Micheal Garcia, ya ce boye bayanai da nufin kassara wani bincike na karya kashin bayan duk wata hukuma.

Garcia ya yi wannan batun ne a lokacin da shugaban FIFA Sepp Blatter yake shan suka kan kin amincewa a wallafa binciken cin hanci ga kasar da za ta karbi bakuncin kofin duniya na shekarar 2018 da 2022.

Garcia ya kara da cewa hukumar FIFA tana gudanar da wasu aikace-aikacenta ba tare da sanin halin da ake ciki a ko yadda ake gudanar da ayyuka ba.

Lauyan ya ce sai an bi doka da oda za a samu kwarin gwiwar shugabanci a tsarin hukumar da amince wa juna daga masu bibiyar aikin hukumar da kuma masu sha'awar kwallon kafa.