Kluivert ya fice daga masu zawarcin kocin Ghana.

Bernd Schuster
Image caption Bernd Schuster na fatan samun damar horas da Ghana

Bernd Schuster ya maye gurbin Patrick Kluivert a cikin kociyoyi biyar dake son aikin horas da tawagar 'yan kwallon Ghana.

Hukumar kwallon kafar Ghana ta ce Kluivert dan kasar Nehterlands, ya janye daga cikin masu son maye gurbin Kwesi Appiah ne don radin kansa.

Sauran kociyoyin da suke cikin takara sun hada da tsohon kocin Chelsea Avran Grant da Marco Tardelli da Micheal Pont da Juan Ignacio Jimenez.

Hukumar kwallon Ghana ta shirya tattauna wa da Kluivert ranar 17 ga watan Oktoba, kafin ya janye daga cikin 'yan takarar.

Hukumar za ta gana da Pont da Tardelli ranar 17 ga watan Oktoba, sannan ta tattauna da Grant da Jimenez ranar 18 ga watan Oktoba a Accra.

Ghana ta tashi wasa 1-1 da Guinea a karshen mako a wasan neman tikitin shiga kofin Afirka, inda Maxwell Konadu ne ya jagoranci tawagar 'yan wasan a matsayin kocin rikon kwarya.