Keshi ya ce zagon kasa ake yi wa Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ya ce abin kunya ne, yadda masu zagon kasar ba sa son ganin Nigeria ta je gasar cin kofin Afirka a shekara mai zuwa

Kocin Nigeria, Stephen Keshi ya yi ikirarin cewa ana yi wa kokarin kungiyarsa Super Eagles na samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekara mai zuwa zagon kasa.

A ranar Asabar ne, Nigeria ta yi wata wawar rashin nasara da ci 1 mai ban haushi a hannun Sudan, inda a yanzu take kasan rukuni na 1 da maki guda rak.

Nigeria dai tana fama da matsaloli da dama da suka hadar da rikicin shugabancin Hukumar kwallon kafar kasar, ga shi kuma Keshi na aiki ba tare da kwantiragi ba.

Keshi ya ce ba zai ambaci suna ba, amma wasu mutane suna yi musu zagon kasa, kuma sun san kansu.

Ya ce mutanen a shirye suke su sayar da mutuncin Nigeria kan dan abin da za su samu. Ya ce ba sa son ci gaban kungiyar Super Eagles.