Wenger ya yi nadamar ture Mourinho

Arsene Wenger sorry Mourinho. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger ya ce an fifita labarin laifin da ya aikata da yawa

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce yi yi nadama da ya hankade Jose Mourinho a karawar da Chelsea ta doke kungiyarsa da ci 2-0 a cikin watannan.

Wenger ya ture Mourinho ne a lokacin da ya shiga da'irirar da mai horas da Chelsea yake tsaye a wasan Premier a filin Stamford Bridge ranar 5 ga watan Oktoba.

Wenger mai shekaru 64 ya fada a wata kafar yada labarai cewa "An fifita labarin laifin da ya yi, wanda bai kamata ya aikata hakan ba".

Kocin Arsenal ya harzuka a lokacin da Gary Cahill ya yiwa dan wasan Arsenal Alexis Sanchez keta, sai dai bayan an tashi wasa yace ba zai nemi afuwar laifin da ya aikata ba.

Hukumar kwallon kafa ba za ta dauki mataki akan Arsene Wenger ba.