Zambia ta kori kyaftin din ta Katongo

Chris Katongo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kyaftin din ya samu sabani da kociyoyin zambia ne

Zambiya ta sallami kyaftin din ta Chris Katongo daga tawagar 'yan wasan kwallon kafar kasar da suke shirin karawa da Niger a wasan neman tikitin shiga gasar kofin Afirka.

Kotongo ya bar sansanin horas da 'yan wasan Zambia bayan da suka sami sabani tsakaninsa da masu horas da tamaula.

Kyaftin din ya sanar da BBC cewa ya bar filin atisaye dake Ndola, amma bai yi cikakken bayani ba.

Kotongo ya buga wasan da suka tashi da Niger canjarasa a ranar Asabar, inda ya sauya dan kwallo a minti na 76.

Tsohon fitatcen dan kwallon kafa da BBC ke karramawa duk shekara, ya jogoranci Zambia lashe kofin Afirka da Gabon da kuma Equatorial Guinea suka karbi bakunci