Argentina ta doke Hong Kong da ci 7-0

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Argentina ta hushe haushinta ne a kan Hong Kong

Argentina ta doke Hong Kong da ci 7-0, inda Lionel Messi ne ya zura kwallaye biyu a wasan sada zumunci da suka buga.

Messi mai wasa a Barcelona wanda ya canji dan kwallo, shi ne ya zura kwallo ta biyar data shida a raga.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci dan wasan Sevilla Ever Baneg ne ya fara zura kwallo, sai Gonzalo Higuain ya kara ta biyu da kai, kafin Nicolas Gaitan ya kara kwallo ta uku a raga.

Bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne Higuain da Gaitan suka kara kwallayensu na bibiyu a raga.

Argentina ta huce fushinta ne akan Hong Kong bayan da ta yi rashin nasara a hannun Brazil da ci 2-0 a wasan sada zumunci da suka buga a Beijing ranar Asabar