Da wuya a maye gurbin Wenger - Gazidis

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger yanzu shi ne wanda yafi dadewa a kocin Premier

Shugaban kungiyar Arsenal Ivan Gazidis ya ce da wuya a samu kocin da zai maye gurbin Arsene Wenger idan har ya bar kulob din.

Wenger, wanda zai cika shekaru 65 ranar 22 ga watan Oktoba, ya sabunta kwantiraginsa na tsawon shekaru uku a watan Mayu.

Gazidis ya ce kalubalen dake gabansu shi ne samun magajin Wenger duk lokacin da ya bar Arsenal.

Wenger ya jagoranci Arsenal buga wasanni 1,023, inda ya lashe wasanni 591, ya yi rashin nasara a karawa 202, sannan ya yi canjaras a fafatawa 230.

Arsenal ta halarci gasar kofin zakarun Turai karo 17 a jere da kuma lashe kofin Premier karo uku karkashin Wenger.

Kulob din ya koma sabon filin wasansa daga Highbury zuwa Emirates a farkon kakar wasan 2006/07, kuma Gazidis ya ce iya matse bakin aljihu da kocin ya yi ne ya bashi damar dauko Mesut Ozil da Alexis Sanchez kan kudi fam miliyan 77.