Super Eagles ta doke Sudan da ci 3-1

Super Eagles
Image caption A watan gobe ne Nigeria za ta bakuncin Congo

Super Eagles ta doke Sudan da ci 3-1 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka a wasan da suka kara ranar Laraba a Abuja, Nigeria.

Nigeria ce ta fara zura kwallo a ragar Sudan minti uku da dawo wa daga hutun rabin lokaci ta hannun Ahmed Musa.

Jimawa kadan Sudan ta farke kwallonta ta hannun Bakry Abdulkadir a minti na 55, kuma shi ne dan wasan da ya zura wa Nigeria kwallo a Sudan a wasan farko.

Super Eagles ta kara kwallo ta biyu ta hannun Aaron Samuel a minti na 65, a wasansa na farko da ya fara buga wa Nigeria tamaula.

Ana kai wa minti na 89 ne Ahmed Musa ya kara kwallo ta uku kuma ta biyu da ya zura a wasan da ya bai wa Super Eagles damar lashe maki uku.

Nigeria mai rike da kofin Nahiyar Afirka tana da maki hudu kenan a wasanni hudun data buga, yayin da Sudan ke da maki uku.