Birtaniya ta damu da tsadar kallon kwallo

Arsenal ticket Price.
Image caption Tashin gwauron zabi a kudin tikitin kallon tamaula

Birtaniya ta damu da tashin gwauron zabi da tikitin kallon kwallon kafar kasar keyi, har ma ta umarci kungiyoyin da suyi bitar tsadar shiga filayen wasanninsu.

Ministan wasanni Helen Grant ta shaida wa BBC cewa: "Ina ganin kungiyoyin kwallon kafa suna son su raina hankalin masu kallon wasa ne"

Matsakaicin tikitin kallon wasa mafi sauki a Birtaniya, ya lunka tsadar rayuwa har kashi biyu tun daga 2011.

Hakan yasa an samu karin kaso 13 cikin dari tun daga 2011, idan aka kwatanta da karin tsadar rayuwa da ya kai kusan kaso bakwai cikin dari.

Ana sa ran kungiyar magoya bayan Arsenal za su bukaci kulob din ya rage kudin shiga kallon wasanninta a taron da za su gudanar ranar Alhamis.

A binciken da aka gudanar kan tsadar kallon tamaula, Arsenal ce kan gaba wajen tsadar tikitin shiga kallon wasan Premier ta.