UEFA: Tana tuhumar Serbia da Albania

Serbia vs Albania Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karawar da aka raba raini tsakanin Serbia da Albania

Hukumar kwallon kafar Turai tana tuhumar Serbian da Albanian kan yamutsi da ya haddasa dakatar da karawar da su ka yi a wasan neman tikin shiga gasar cin kofin Turai.

'Yan wasa da magoya bayan kasashen biyu sun bai wa hammata iska a Belgrade, bayan da wani jirgin sama ya zagaya filin wasa dauke da kyalle mai sakon goyon bayan Albania.

Hukumar UEFA tana tuhumar Albania kan kin komawa wasa, bayan da alkalin wasa ya umarta aci gaba da wasa, da kuma hayar jirgin da ya haddasa yamutsi a karawar.

Ita kuwa Serbia ana tuhumarta da laifuka guda biyar da ciki har da kasa kwantar da tarzoma a lokacin da yamutsin ya barke.

Kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon Turan ya tsaida ranar 23 ga watan Oktoba domin sauraren jin bahasin kasashen biyu.