Ingila:Lineker na so a bai wa matasa dama

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lineker ya ce matasa za su taka rawar gani

Gary Lineker ya bukaci jami'an gasar Premier ta Ingila su bai wa yara 'yan kasa da shekaru 21 dama a cikin gasar domin nuna bajintarsu.

Lineker yana so yaran da suka kware 'yan Burtaniya su shiga a fafata da su a gasar cin kofin Turai da za a buga a watan Yuni mai zuwa.

Shugaban Everton Roberto Martinez ya gargadi Ingila cewa kada ta zabi Ross Barkley cikin 'yan wasan da za su yi mata wasa.

Tsohon dan wasan na Ingila, kuma mai ba da labaran wasanni ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, " Ya kamaya duk 'yan kasa da shekaru 21 su fafata a wasan karshe na kakar wasa ta badi idan har sun cancanta. Sauran kasashe suna tabbatar da hakan".

Karin bayani