Athletico Madrid ta lashe wasanni 24 a gida

Athletico Madrid Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Athletico Madrid ce ke rike da kofin La Ligar Bara

Athletico Madrid ta tsawaita lashe wasanninta har 24 a gida, bayan da ta doke Espanyol 2-0 a gasar La Liga wasan mako na takwas da suka buga ranar Lahadi.

Athletico ta fara zura kwallo ta kafar Tiago Mendes ana saura minti biyu a tafi hutu, kafin ta kara ta biyu ta kafar Mario Suarez a minti na 71.

Espanyol ba ta samu damar zura kwallo a ragar Athletico ba, kuma kiris ya rage Antoine Griezmann ya kara jefa mata kwallo ta uku .

Nasarar da Athletico ta samu tasa Barcelona wadda ke matsayi na daya a teburi ta ba ta tazarar maki biyar.

Rabon da Athletico ta yi rashin nasara a wasan gida tun fafatawar da Barcelona ta doke ta 2-1 ranar 12 ga watan Mayu.