Da kyar idan Bale zai buga karawa da Liverpool

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gareth Bale ya buga wa Madrid wasanni 12 a bana

Dan kwallon da Real Madrid ta sayo mafi tsada a duniya Gareth Bale kila ba zai buga karawar da za suyi da Liverpool a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba ba.

Bale, mai shekaru 25, ya ji rauni a kafarsa, kuma ba a saka shi a wasan da Madrid ta doke Levante ranar Asabar ba.

Wani rahoto da Madrid ta fitar bai bayyana kwanakin da zai yi jinya ba, illa dai sun ce suna duba girman raunin da ya ji.

Liverpool za ta karbi bakuncin Madrid a wasan 'yan rukuni na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai, kafin su fafata da Barcelona ranar Asabar.

Bale ya buga wa Wales wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da suka kara da Bosnia-Hercegovina ranar 10 ga watan Oktoba da kuma Cyprus kwanaki uku tsakani .

Dan kwallon ya buga wa Madrid wasanni 12 a bana, inda ya zura kwallaye biyar a raga.