'Kada a saka dogon buri da Super Eagles'

Shuaibu Amodu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amodu ya ce zai yi kokarin kai Super Eagles gasar kofin Nahiyar Afika

Kocin Super Eagles Amodu Shaibu ya ce kada 'yan Nigeria su saka dogon buri akan tawagar 'yan kwallon kasar duk da alkawarin da ya yi na zai kai kasar gasar cin kofin Nahiyar Afirka.

Shuaibu wanda zai gudanar da aiki tare da Salisu Yusuf da Gbenga Ogunbote da Alloy Agu an basu alhakin kai Nigeria wasan kofin Afirka na badi.

Kocin ya ce "An hada mu da aiki mai dan karen wahala, amma za muyi iya kokarinmu domin Super Eagles ta kare kambunta a watan Janairu mai zuwa".

Ya kuma kara da cewa Nigeria na cikin tsaka mai wuya, musammam yadda 'yan kasa suka dora burin Nigeria ta kare kambunta duk rintsi.

Nigeria tana mataki na uku a rukunin farko da maki hudu, wadda take biye da Cogo a mataki na biyu sai Afirka ta Kudu a matsayi na daya.