West Brom da Man. United sun tashi 2-2

West Brom vs United Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption West Brom da Manchester vUnited sun raba maki guda kowannen su

Manchester United ta tashi wasa 2-2 a karawar da suka yi a gidan West Brom a gasar cin kofin Premier wasan mako na takwas.

West Brom ce ta fara zura kwallo a ragar United ta hannun Stephane Sessegnon, bayan da aka dawo daga hutu Marouane Fellaini ya farke wa United kwallo.

Saido Berahino ne ya kara kwallo ta biyu a ragar United, kafin daga baya Blind ya farke wa United, bayan da kwallo ta bugi turki daga bugun Robin van Persie.

United tana matsayi na shida a teburin Premier da maki 12, yayin da West Brom ta gusa zuwa mataki na 14 da maki tara.