AFCON 2015: Afirka ta kudu ta ce a kai kasuwa

Fikile Mbalula Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Afirka ta Kudu ta ce bata shirya karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka ba

Ministan wasannin kasar Afirka ta Kudu Fikile Mbalula ya ce kasarsa ba za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Nahiyar Afirka ba, idan Morocco ta janye.

A makon jiya ne hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta yi wa kasar Afirka ta Kudu tayin karbar bakuncin gasar, bayan da Morocco ta bukaci a dage wasan saboda cutar Ebola.

Mbalulu ya fada a wata kafar yada labarai ce wa "Ba za mu karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka ba, bamu da kudin shirya karbar bakuncin wasannin a yanzu".

Afirka ta Kudu tana daga cikin kasashe takwas da CAF ke hangen za ta iya maye gurbin Morocco wadda ta bukaci a dage wasannin da za'a fara daga 17 ga watan Janairu badi.

Sama da mutane 4,500 ne suka mutu sakamakon cutar Ebola wadda ta mamayi Afirka ta yamma tun farkon shekarar nan.