Labaran da suka fi jan hankali a Premier

Poyet Koeman Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Labaran da suka fi jan hankali a gasar Premier bayan buga wasannin mako na 8

Van Gaal ya yi na'am da ci gaban United

Louis van Gaal ya ce bai kamata a fara yabonsa watanni uku da fara aiki a kofin Manchester United ba. Bayan da suka tashi wasa da West Brom 2-2 a gasar Premier, har yanzu magoya bayan kulob din na fatan fara lashe wasan farko a waje a bana. Van Gaal ya yabi United da taka rawar gani a karawar, duk da kulob din yana mataki na shida a teburin Premier, kocin ya ce har yanzu akwai jan aiki a gabansu.

Akwai Shakku a karfin 'yan bayan Liverpool

Liverpool wadda ta kare gasar Premier bara a matsayi na biyu da kyar ta doke QPR 3-2, inda aka zura kwallaye hudu saura mintuna takwas a tashi wasa. Nasarar da Liverpool ta samu yasa ta gusa zuwa mataki na biyar a teburin Premier, yayin da QPR ta fada matsayi na karshe a teburi bayan buga wasanni takwas. Sai dai akwai shakku ga 'yan bayan Liverpool ta yadda suka bari aka zura musu kwallaye biyu da kuma ruwan hare-hare. Kocin QPR yayi korafin rashin dan wasansa mai zura kwallo a raga Adel Taarabt wanda ya ce yayi nauyi dalilin da yasa bai buga karawar ba - Dan wasan ya karyata zargin.

Monk ya harzuka da fenaritin Moses

Kocin Swansea Garry Monk ya bayyana nasarar da Stoke ta samu a kansu da yin Magudi, bayan da Stoke ta samu fenariti a ketar da aka yi wa Victor Moses aka doke su 2-1 a filin wasa na Britannia. Monk ya ce ya kamata Moses ya yi Allah wadai da dabi'ar da ya nuna a lokacin da ya fadi cikin da'ira ta 18 bayan da suka yi taho mu gamu da mai tsaron baya Angel Rangel. Kocin Stoke Mark Hughes ya ce bai ga wani laifi da Moses ya yi ba, har ma ya ce ba za su amince da kalaman Monk ba.

Wenger ya yi korafin rashin 'yan baya

Kocin Arsenal Arsene Wenger yana daga cikin kociyoyin da basu ji dadin sakamakon wasan mako na takwas ba, har ma ya soki Jacqui Oatley mai rahotan BBC, bayan da suka tashi wasa 2-2 da Hull City. Wenger ya zargeta da kin saurarensa da kuma kokarin ganin laifin wasu, bayan data tambaye shi dalilin da yasa Arsenal wasanni biyu ta lashe daga cikin wasanni takwas da ta buga a bana. Arsenal tana mataki na bakwai a teburin Premier kuma kocin yana sane da haka, ba dan Danny Welbeck ya farke kwallo daf a tashi wasa da labarin bai yiwa Arsenal dadi ba a Emirates.

Koeman ya yi murnar lallasa Sunderland

Ronald Koeman sabon koci ne a gasar Premier bana da ya fara gasar da kafar dama a kulob din Southampton. Tun zuwansa kulob din ya dauko sabbin 'yan kwallo wadanda ya gauraya da tsoffin 'yan wasa suke kuma buga salon kwallo mai ban sha'awa. Hakan ne ma yasa suka casa Sunderland 8-0 a wasan da aka fi ruwan kwallaye a raga a gasar Premier bana, kuma wasan ne aka kafa tarihin wanda ya fi yawan zura kwallo a tarihin gasar Premeir.