Na bar United da martabarta - Ferguson

Ferguson Moyes Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ferguson ya ce Moyes bai san United tana da girma ba

Alex Ferguson ya kare kansa bisa zargin da ake masa cewar 'yan wasan Manchester United basu da inganci a lokacin da ya bai wa David Moyes gadon kulob din.

A lokacin da ya sabunta bayanan da ya wallafa littafin rayuwarsa na 2013, ya ce shi da kansa ya zabo Moyes ya gaje shi ba tilasta masa shi aka yi ba.

Ferguson wanda ya yi ritayar horas da United a shekarar 2013 ya ce bai kamata a ce 'yan wasan kulob din basu da inganci lokacin da ya bar United ba.

United ta sallami Moyes a cikin watan Afirilun 2014, bayan da ya jagoranci kulob din watanni 10, inda suka kare a matsayi na bakwai a teburin Premier.

Ferguson ya maida martani kan cewa ya bar kulob din da tsoffin 'yan wasa, inda ya ce United ce ta lashe kofin Premier a shekarar 2012/13 da tazarar maki 11, kuma 'yan wasa 11 daga cikinsu suna da shekaru kasa da 25.