Sunderland za ta biya magoya bayanta kudin tikitinsu

Southampton Sunderland Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan kulob din na fatan huce haushi a kan Arsenal a Premie

Kulob din Sunderland zai biya magoya bayansa wadanda suka ziyarci filin wasa na Southampton a karawar da aka doke su 8-0 a gasar Premier ranar Asabar.

Tun farko Golan kulob din Vito Mannone ne ya bayar da shawarar a biya magoya bayan kulob din kudin zirga-zirgar abin hawa da kudin shiga kallon wasan.

Sunderland ta sanar a shafinta na Intanet cewa 'yan wasanta sun amince su biya magoya bayansu kudin dawainiyar da suka yi a karawar da aka casa su a Southampton.

Ana tunanin 'yan wasan za su biya kimanin fam 60,000 ga magoya baya su 2,500 da suka halarci filin wasa na St Mary ranar Asabar.