Warri Wolves ta casa Crown FC da ci 7-0

NFF Logo
Image caption Saura wasanni uku a kare gasar Premier Nigeria

Kungiyar kwallon kafa ta Warri Wolves ta doke Crown FC da ci 7-0, a gasar cin kofin Nigeria Premier wasannin mako na 35 da suka buga ranar Laraba.

Sauran sakamakon wasanni da aka fafata, Kano Pillars ta doke Kaduna United da ci 2-1 a karawar hamayya, inda Enyimba ta doke El -kanemi Warriors da ci daya mai ban haushi.

A fatakwal kuwa Nembe City dauko kwallaye shida da ba ko daya ta yi a wajen Dolphins, Sunshine Stars ta samu nasara akan Gombe United da ci 2-0.

Har yanzu Kano Pillars ce take matsayi na daya da maki 62 a teburin Premier Nigeria, yayinda Warri Wolves ke mataki na biyu da maki 61.

Ga sakamakon wasannin mako na 35 da aka buga:

Abia Warriors 1-1 Heartland Akwa United 1-0 Bayelsa United Dolphin 6-0 Nembe City FC Enugu Rangers 1-0 Sharks Enyimba FC 1-0 El-Kanemi Warriors Kano Pillars 2-1 Kaduna United Sunshine Stars 2-0 Gombe United Taraba FC 2-0 Lobi Stars Warri Wolves 7-1 Crown FC