'Zan kai Super Eagles Gasar Cin Kofin Afirka'

Saibu Amodu
Image caption Wannan ne karo na biyar da Amodu ke horar da Nigeria

Shaibu Amodu na fatan sama wa Nigeria gurbin a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka a badi, duk da Super Eagles tana cikin tsaka mai wuya.

Amodu ya maye gurbin Stephen Keshi ne a makon jiya, bayan da tsohon kocin ya kasa taka rawar gani a wasannin neman tikitin gasar.

Nigeria, wadda ke rike da kofin, tana mataki na uku a rukunin farko da maki hudu, inda Afirka ta Kudu ke matsayi na daya, sai Congo a matsayi na uku.

Amodu ya ce "An ba mu aiki mai wahala wanda yake cike da kalubale, sai dai kuma babu abin da zai gagara, za mu yi iya kokarinmu".

Wannan ne karo na biyar da Amodu ya karbi aikin horar da Super Eagles, kuma zai jagoranci tawagar zuwa Congo a wasa na biyu da za su buga ranar 15 ga watan Nuwamba.