Platini ya bukaci CAF ta nemi gafararsa

Michel Platini Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Platini ya ce an yiwa jawabin nasa mummunar fahimta

Shugaban hukumar kwallon kafar Turai UEFA, Michela Platini ya bukaci CAF ta nemi afuwarsa, bayan data caccake shi akan jawabin da yi yi kan karbar bakuncin kofin Afirka.

CAF ta zargi Platini da kokarin yin zagon kasa da shiga zarafin da bai shafe shi ba, bayan da ya gama tattauna wa akan tasirin cutar Ebola a gasar Afrika a wata kafar talabijin.

Sai dai kuma shugaban hukumar kwallon nahiyar Turan, Platini, ya ce an yiwa jawabin nasa mummunar fahimta ne.

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF tace ba za ta nemi afuwa daga wajen Platini ba.

An shirya fara gasar cin kofin Nahiyar Afirka a Morocco daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu, daga baya mai masaukin baki ta bukaci a dage wasannin.

Sama da mutane 4,500 ne suka mutu tun lokacin da aka samu barkewar annobar Ebola a Nahiyar Afirka ta Yamma tun daga farkon wannan shekarar.